Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Tabbatar Da Adeleke A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan PDP A Zaɓen Osun

Babbar Kotun Tarayya dake zaman ta Osogbo, Jahar Osun ta kori Ƙarar dake neman ayyana Prince Dotun Babayemi a matsayin Ɗan Takarar Gwamnan a Jam’iyyar PDP a zaɓen Gwamnan Osun na ranar 16 ga watan Yuli.

Kotun ta kuma tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin cikakken Ɗan Takarar da aka zaɓa a zaɓen.

A hukuncin daya yanke wanda ta ɗauki awa ɗaya da mintuna 30, Mai Shari’a Nathaniel Ayo-Emmanuel ya Amince da zaɓen fidda Gwani da aka gudanar a cibiyar WOCDIF, Osogbo a ranar 8 ga watan Maris na shekarar 2022, wanda ayyana Babayemi a matsayin Dan Takara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram