Ƴan bindiga da aka kyautata zaton Masu garkuwa da mutane a ranar Litinin, sun sace Ɗalibai 4 na Kwalejin Ilmi ta Jahar dake Gidan Waya a Ƙaramar Hukumar Jema’a ta Jahar Kaduna.
An sace su ne a yankin Mile 1 na Gidan Waya a ranar Litinin da yamma.
Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Ɗalibai ta Jahar Kaduna, Benjamin Fie a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, yace Ɗaliban an kama su ne a ranar Litinin da yamma a yankin Mile 1.
Fie yace masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su kuɗaɗe masu yawa a matsayin kuɗin fansa kafin su sako su.
Ya karanto sunayen Ɗaliban da suka haɗa da Raheal Edwin Ɗan Aji biyu daga sashen Biology/Geography, da Esther Ishaya, Mai Aji biyu a Sashen Economics, da Sashen History, da Promise Tanimu, ƴar Aji biyu daga sashen English/History, da kuma Beauty Luka, ƴar Aji 300 daga sashen Spe/CRS.
Yace “abin damuwa ne a zuciya na Ƙungiyar Ɗalibai ta Kwalejin Ilmi ta Gidan Waya, muke sanar da Al’umma cewa an kama mutane biyu.
Yace masu garkuwa da mutanen suna neman kuɗin a matsayin kuɗin fansa, yana mai ƙara dacewa “muna Son muyi amfani muyi kira ga Ɗalibai da Al’umma dasu taya su da addu’a.”
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna ASP Mohammed Jalige bai ɗauki kira ba a lokacin da aka kira shi domin jin rahoton.