Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Ƙungiyar Asiri 20 A Benue

Mutane 20 da ake kyautata zaton ƴan Ƙungiyar Asiri ne wanda Rundunar Ƴan Sandan Jahar Benue an kaisu Kotu.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Catherine Anene ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a Makurdi a ranar Alhamis.

Anene ya bayyana cewa an kama ƴan Ƙungiyar Asirin a yankin Wurukum na Babbar Birnin Jahar.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan ya ƙara dacewa turo da Jami’an tsaron ya haifar da Ɗa mai ido, ta hanyar kama wanda ake zargin.

“Ƙoƙarin jami’an tsaron haɗin kai da Jami’an tsaro da al’umma ya sanya an samu zaman lafiya a wuraren, inda aka kama mutane 20 tare da kaisu Kotu.

Anene yayi kira ga Iyaye, Malamai, da masu riƙe da Sarautun gargajiya, da Shuwagabannin Addini dasu haɗa hannu da Jami’an tsaro wajen yaƙi da ƴan Ƙungiyar Asiri a Jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram