Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 360 A Kaduna Cikin Watanni 3 – Kwamishina

Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an kashe mutane 360 ​​tsakanin watan Janairu zuwa Maris 2022 ta hanyar fashin jeji da kuma rikicin ƙabilanci.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da rahoton zangon shekara na farko kan tsaro na shekarar 2022 ga gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, a jiya Alhamis a Kaduna.

Ya ce an yi garkuwa da mutane 1,389 a iya lokacin da aka binciken a yankin Kaduna ta tsakiya.

Aruwan ya ce an yi garkuwa da mutane 169 daga Birnin Gwari, Giwa 158, Igabi 263, Chikun 287 da kuma Ƙaramar Hukumar Kajuru da a ka yi garkuwa da mutane 203.

A cewarsa, akalla mutane 249 ne aka yi garkuwa da su a sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da wasu muggan hare-hare da aka kai a yankin Kudancin Kaduna a dai wannan lokacin da aka yi wannan binciken.

Ya bayyana cewa mutane 258 ne su ka samu raunuka a fadin jihar sakamakon rikicin ‘yan fashi, rikicin kabilanci, yana mai cewa 38 daga cikin wadannan alkaluma mata ne kuma 11 ƴan kasa da shekaru 18 ne.

Aruwan ya ce an sace dabbobi 3,251 a tsawon lokacin, inda 3,137 aka sace daga Kaduna ta Tsakiya, wanda ya kai kashi 97 cikin 100 na adadin. an yi garkuwa da mutane 1,389 a iya lokacin da aka binciken a yankin Kaduna ta tsakiya.

Aruwan ya ce an yi garkuwa da mutane 169 daga Birnin Gwari, Giwa 158, Igabi 263, Chikun 287 da kuma Ƙaramar Hukumar Kajuru da a ka yi garkuwa da mutane 203.

A cewarsa, akalla mutane 249 ne aka yi garkuwa da su a sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da wasu muggan hare-hare da aka kai a yankin Kudancin Kaduna a dai wannan lokacin da aka yi wannan binciken.

Ya bayyana cewa mutane 258 ne su ka samu raunuka a fadin jihar sakamakon rikicin ‘yan fashi, rikicin kabilanci, yana mai cewa 38 daga cikin wadannan alkaluma mata ne kuma 11 ƴan kasa da shekaru 18 ne.

Aruwan ya ce an sace dabbobi 3,251 a tsawon lokacin, inda 3,137 aka sace daga Kaduna ta Tsakiya, wanda ya kai kashi 97 cikin 100 na adadin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram