NRC Ta Dakatar Da Cigaba Da Zirga-zirgar Jiragen Kasa Daga Abuja-Kaduna Sai Baba Ta Gani

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta yi kasa a gwiwa wajen matsin lamba daga iyalan wadanda harin da aka kai kan jirgin Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su a ranar 28 ga watan Maris, yayin da kamfanin zai koma bakin aiki.

A baya dai hukumar ta NRC ta tsayar da ranar Litinin 23 ga watan Mayu domin cigaba da aikin jirgin amma ‘yan uwan ​​wadanda abin ya shafa sun ki amincewa da matakin, inda suka ce babu damuwa a ci gaba da gudanar da aikin a hanyar yayin da ‘yan uwansu ake ci gaba da tsare su.

Da alama dai sun ki biyan bukatarsu, NRC ta dage ci gaba da gudanar da da ayyukan ta sai abunda hali yayi saboda ba a sanar da wata sabuwar rana ba.

Kakakin NRC, Mahmud Yakub, a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ya ce za a sanar da sabuwar rana “nan ba da jimawa ba.”

A cikin sanarwar, NRC ta ba da hakuri kan jinkirin da aka samu na dawo da hidimar duk da cewa ta tabbatar wa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su cewa tana bakin kokarinta wajen ganin ta ceto wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.

Ta ce, “Hukumar NRC za ta ci gaba da ba gwamnatin tarayya hadin kai a kan aikinta na kare martabar yankunan kasa da tsaron cikin gida na Najeriya domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar musamman yadda ya shafi bangaren jirgin kasa.

“Hakazalika, mun sake zayyanawa ‘yan uwan ​​wadanda akayi garkuwa da su saboda harin da aka kai wa AKTS a kwanakin baya domin mu tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na nan a raye domin daukar nauyi na ceto duk mutanen da akayi garkuwa da su.

“Don haka muna kira, musamman ga ‘yan uwan ​​wadanda aka yi garkuwa da su da su yi hakuri tare da bayar da hadin kai ga Hukumar da Hukumomin tsaro domin Gwamnatin Tarayya na lalubo hanyoyin da za a bi don ganin an kubutar da ‘yan uwansu daga garkuwar da akayi dasu cikin gaggawa.

“NRC na nuna matukar godiya ga jami’an tsaro saboda ci gaba da tallafawa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram