Ahmed Lawan Ya Gana Da Wakilan Jam’iyyar APC Masu Zaɓen Ƴan Takara A Katsina

Shugaban majalisar dattawan Kasar nan Sanata Ahmad Lawan ya ce ba gaskiya a batun da ake cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya samu koma baya kan nasarorin da ya fara samarwa.

Sanata Ahmad Lawan wanda guda ne cikin masu son tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC ya ce sun yadda cewa akwai wasu wurare da ya gaza, a dan haka zasu mayar da hankali wajen ganin sun Waiwayi wannan waje da nufin samar musu da abubuwan da suke da bukata.

A cewar Lawan matsalar tsaro a wasu yankuna na daga cikin kalubalen da Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari ya ke fuskanta, a dan haka yace a 2023, zasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun magance wannan matsala.

Shugaban majalisar na jawabi ne a Jiya, yayi. Da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar APC masu zaben fidda gwani, a jihar Katsina, wadanda yake gare su da nufin neman yardar su domin tsayar da shi a matsayin wanda suke fatan ya gaji kujerar Buhari.

Ya ce kuma ganawarsa da wakilan jam’iyyar APC na jihar Katsina itace ta farko da yayi, tun bayan da ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram