Amaechi Ya Fara Kamfen Da Talaucin Gidan su, A Ƙoƙarin Sa Na Zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A APC

Tsohon ministan sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi ya ce yanzu haka Kasar nan shi tafi bukata saboda shine talaka kuma ya fito daga tsatson Talakawa.

Amaechi wanda guda ne cikin masu Zawarcin Kujerar Shugaba Buhari, ya bayyana taron wakilai masu zaben fidda gwani cewa, cikin yan takarar shugaban kasa yafi kowa cancanta.

A cewar sa saboda halin talauci da suke fama da shi, ya kan sha Garri sau uku a rana, tsawon lokaci ba tare da ya damu ba, saboda sabon da suka yi da Garri.

Tsohon ministan na wannan jawabi ne domin neman goyon bayan wakilan, wajen zabar sa a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, yayin zaben 2023.

Yanzu dai a iya cewa bayan gaza gamsuwa da bayyana irin matsayin da mutum ke da shi, ta kai ga fara Yakin neman zabe ta hanyar amfani da talauci.

Amaechi ya kuma ce yanzu lokaci ne da ya kamata yan Kasar su tashi tsaye, domin dai zaban cancanta don gudun sake fadawa hannun yan baba-kere.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram