Babu Sauran Nadama Idan Har Ƴan Najeriya Suka Same Ni A Matsayin Shugaban Ƙasa – Tinubu

‘Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa ba za su yi nadama ba idan suka sameni a matsayin shugaban kasa a 2023.

Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar Kano gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Tun ranar Alhamis ne Tinubu yake Kano.

Ya sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) inda magoya bayansa suka tarbe shi.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da wasu ministocinsa da kuma shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Abbas ne suka karbi bakoncin dan takarar shugaban kasa na farko a hukumance.

Tinubu, a cikin wani dogon ayari, an raka shi zuwa gidan hamshakin dan kasuwa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, da tsohon abokinsa kuma abokin siyasarsa, Alhaji Yusuf Ali, inda suka yi takaitacciyar tattaunawa da dattawan biyu kan kudirinsa na shugaban kasa.

Daga gidan Yusuf Ali, Tinubu ya zarce zuwa dakin wasanni na cikin gida na Sani Abacha Stadium.

A filin wasan, tsohon Gwamnan Legas ya gana da dimbin magoya bayansa da suke jira.

Daga filin wasa ya tashi zuwa gidan gwamnati Kano, ya kuma yi doguwar ganawa da wakilai a dakin taro na Coronation Hall.

Yayin da yake zawarcin wakilan Kano, shugaban jam’iyyar ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata a mara masa baya domin ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

“Ina kira gare ku da ku goyi bayan burina na shugaban kasa. Ku zabe ni don samun tikitin jam’iyyar a zaben fidda gwani mai zuwa.

“Yau ce ranar da na zo neman goyon bayan ku don zama shugaban Najeriya. Kuna iya sanya ni a can tare da kuri’un ku.

“Na yi imani da kaina. Ni mai wayo ne, haziki da jaruntaka, kada ka yi kuskure, ka zaba cikin hikima, ka zabe ni, ina rokonka, kuma ba za ka taba yin nadamar goyon bayana ba,” in ji Tinubu.

Tinubu ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro, farfado da tattalin arziki, bunkasa noma tare da inganta ababen more rayuwa.

Ganduje ya ce Tinubu ya yi wa jam’iyya mai mulki hidima kuma lokaci ya yi da za a biya shi.

Gwamnan ya jaddada cewa: “Tinubu ya sadaukar da yawa don ci gaba da hadin kan APC. Tinubu ya kasance tambarin jagoran Najeriya da ‘yan Najeriya ke bukata a wannan lokaci na tarihin kasar. Tinubu yana da hankali da siyasa don sake mayar da kasar nan da kuma bai wa ‘yan Nijeriya shugabanci nagari.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram