Ana zargin jima wani Fasto rauni tare da ƙona Gidaje da dama daga Matasa, sakamakon zargin yin ɓatanci a yankin Katangan na Ƙaramar Hukumar Warji ta Jahar Bauchi.
Har yanzu babu cikakken bayani akan yadda lamarin yake, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Wakilin Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ya gano cewa, wannan rikici ya ɓarke ne bayan wani saƙo ya watsu, da wata Yarinya Kirista a garin ta yi ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.
Wata Majiya ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa “dagaske ne lamarin ya faru. Duk wannan abun ya faru ne saboda zargin ɓatancin da Deborah tayi na Sokoto a satin daya gabata.
“Abinda na gano cewa shine, akwai wata yarinya Mabiya Addinin Kiristanci data tura saƙo tana magana akan wani abu a Kafafen Sadarwa na Zamani, wanda yana da nasaba da lamarin da ya faru a Sokoto, wannan shine abinda faru.
“Wannan lamari ya wuce yanda ake zato, tunda har an ƙona gidaje. Amma ba’a rasa rai ba, a iya sani na.
“Wani shago na Cocin ECWA a yankin shima an ƙone shi. Kuma na gano cewa Shuwagabannin yankin sun goyi bayan haka. An sanar da Ƴan Sanda akan hakan.”
Wata Majiyar tace “muna gida da safe muka ji wasu Musulmi da yawansu suka ƙona Cocin ECWA dake yankin, amma Kiristoci sun rama harin da suke zargin an kawo masu, amma wannan ya faru ne bayan sun ƙone shago, kuma Matasan sun ƙone Gidaje da dama.
Ɗaya daga cikin Shuwagabannin Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya a Jahar, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Ƴan Jarida ta wayar tarho.
Yace Kwamishinan Ƴan Sandan Jahar da Babban Mai Taimakawa Gwamnan Jahar Bauchi kan Kiristoci duk sun san da faruwar lamarin.
Yayi kira ga Kiristoci da kada su bari wannan hatsaniyar da fantsama zuwa wasu wuraren.
Duk ƙoƙarin da aka yi na jin tabakin Rundunar Ƴan Sandan Jahar Bauchi bai samu ba, domin an kira Mai Magana da Yawun Rundunar Ahmed Wakil, amma bai ɗaga kira, ko maido wa ba.