Daliban Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna (KSCOE), Gidan Waya da aka yi garkuwa da su kwanaki uku da suka wuce, sun samu ‘yanci.
Daliban dai sun haɗar da Racheal Edwin, Esther Ishaya, Promise Tanimu, da Beauty Luka baki dayan su a karamar hukumar Jemaá ta jihar.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su makudan kudade, kamar yadda Comrade Benjamin Fie, shugaban kungiyar dalibai a makarantar ya bayyana.
“Tuni wadanda suka yi garkuwa da su suka bukaci a biya su makudan kudade domin a sako su.
Muna so mu yi amfani da wannan kafar wajen jawo hankalin al’ummar kwalejin da daukacin daliban da su jajirce wajen yin addu’o’i, makarantar da iyayensu,” inji shi.
Fie bai bayyana ba cewa an biya wani kudin fansa, ko akasin haka, Sai dai ya ce an garzaya da su asibitin tunawa da Sir Patrick Ibrahim Yakowa da ke garin Kafanchan domin duba lafiyarsu bayan sun hadu da ‘yan uwansu.