EFCC Ta Saki Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilai, Patricia Etteh

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayar da belin tsohuwar kakakin majalisar wakilai, Misis Patricia Olubunmi Etteh.

An sake ta a daren jiya Juma’a bayan da ta cika sharuddan belin da masu bincike da ke aiki kan karar ta suka yi mata.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce tsohonwar shugaban majalisar zata kai Kanta ofishin hukumar lokaci bayan lokaci domin taimakawa wajen gudanar da bincike.

Idan za’a iya tuna cewa an kama ta ne a ranar 17 ga Mayu bisa zargin ta da hannu a karkatar da wasu Makudan kudade tare da kamfanin Phil Jin Projects Limited.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta NDDC ta ba Phil Jin Projects Limited kwangilar samar da fitilun titi masu amfani da hasken rana a wasu al’ummomi dake jihar Akwa Ibom.

Kamfanin ya karbi Naira Milliyan 287, duk da cewa kwangilar ta kai Naira Milliyan 240m.

Daga baya Phil Jin Project Ltd ya biya Naira Milliyan 130 ga Patricia Etteh.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa na gudanar da bincike domin gano dalilin da ya sa tsohuwar ministar ta karbi kudin alhali ita ba darakta ba ce a kamfanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram