Kalaman Ɓatanci Ga Annabi SAW: Ƴan Sanda Sun Tabbatar Da Ƙone Gidaje 6, Shaguna 7 A Bauchi

 

Rundunar Ƴan Sandan Jahar Bauchi ta tabbatar da jin raunuka ga mutane da dama, a yayinda aka ƙona gidaje 6 da Shaguna 7 a Ƙaramar Hukumar Warji kan rikicin daya ɓarke sakamakon zagin Annabi Muhammad SAW.

Dayake jawabi kan musabbabin abinda ya janyo rikicin, Kwamishinan Ƴan Sanda na Jahar Umar Mamman Sanda yace wani saƙo na ɓatanci da aka tura a Kafafen Sada Zumunta na Zamani da wata Rhoda Jatau mai shekaru 40, dake aiki a Sashen kula da lafiya na Ƙaramar Hukumar Warji tayi, shine ya haddasa rikicin.

Yace tuni an tura ƴan sanda ƙwararru, da Mobayil domin ganin sun shawo kan wannan rikici.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Mohammed Wakil, a cikin wata sanarwar daya fitarwa Manema Labaru yace Kwamishinan Ƴan Sanda ya bada umarnin a yi bincike akan rikicin.

Ya ƙara dacewa, Kwamishinan ya kuma yi kira ga Shuwagabannin Addini dana Al’umma dasu riƙa gayawa illar yin duk wani abu dazai kawo tsaiko ga sha’anin tsaro a yankunan.

Sanarwar tace “a ranar Juma’a 20 ga watan Mayu na shekarar 2020, da misalin ƙarfe 5:45 wasu Matasan Irate Suka ƙona gidaje 6 da Shaguna 7, a yayinda wasu suka ji raunuka, a dalilin kalaman Ɓatanci da wata Rhoda Jatau tayi mai shekaru 40 dake aiki da Sashen kula da lafiya na Ƙaramar Hukumar Warji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram