Sare kan Ɗan Majalisa na Anambra Ikechukwu Okoye an bayyana shi a matsayin rashin bin Doka tsantsa dake cigaba da yaɗuwa a Najeriya.
An gano kan Okoye ba tare da gangar jikin sa ba a ranar Asabar a Nnobi na Ƙaramar Hukumar Idemili ta Jahar Anambra, kwanaki bayan sace shi.
Dayake maida jawabi akan wannan mummunan lamari, Shehu Sani ya bayyana hakan a matsayin abun damuwa, kuma abun Allah wadai.
A cewar sa, irin wannan mummunan kisa, ya nuna cewa akwai rashin bin Doka tsantsa dake cigaba da yaɗuwa a dukkanin sassa na Najeriya.
Tsohon Sanatan yayi wannan jawabin a shafin sa na Twita, “Sare kan Ɗan Majalisa okechukwu Okoye da ƴan ta’adda suka yi abin Allah wadai ne.
“Kuma hakan ya nuna cewa rashin Doka yana cigaba da fantsama a dukkanin sassan Ƙasar”.
Haka zalika, Gwamnan Jahar Anambra Farfesa Charles Soludo ya sanya tukuicin Naira Miliyan 10 ga duk wanda ya gano makasan Okoye.