Ganduje Ya Raba Miliyan 16 Ga Iyalan Waɗanda Fashewar Bom Ya Rutsa Da Su

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya raba kudi naira miliyan 16 ga iyalan wadanda fashewar Bom ɗin Sabon Gari ya shafa.

Rabon ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar Kano, bayan an tattaro iyalan wadanda lamarin ya shafa, nufin rage musu radadin halin da suke ciki.

Gwamnan ya jagoranci mika kudin ga iyalan mutum tara da suka rasa ransu naira miliyan kowannen su, inda kuma aka baiwa mamallakin ginin Kulop din D African Center naira miliyan biyu, wanda shima abun ya gida da wani bangare na ginin nasa.

Kazalika shina mamallakin makarantar Winners Primary School ya rabauta da tallafin naira miliyan guda, da nufin shima ya tare wani bangare na barnar da ta faru.

Haka zalika mutane goma da suka samu munanan raunuka aka basu naira dubu dari biyu kowannen.

Da yake jawabi kan makasudin bayar da tallafin, gwamna Ganduje, yace an bada tallafinne domin ya ragewa iyalan wadanda abin ya shafa radadin da suke ciki

Ya kuma jajantawa iyalan bisa abun tausayin da ya faru gare su, tare da addu’ar Allah ya kiyaye gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram