Bayan Kashe Uwa Da Ƴaƴanta 4, Da Wasu Ƴan Arewa 6, Kullum IPOB Sai Sun Kashe Mu A Anambra – Sarkin Hausawa

Jami’an Ƙungiyar Ƴan Ta’addan ta IPOB a ranar Lahadi sun kashe wata Mata, da ɗiyanta 4 da wasu guda 6, dukkanin su ƴan Arewa ne a Jahar Anambra, Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Matar wadda ta kasance tana da ciki, sun kashe ta tare da ɗiyan ta a Isulo, Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa ta Jahar.

Kisan ya nuna ƙaruwar aikata Kashe-kashe da ƴan Ta’addan IPOB suke yi ga Hukumomin tsaro na Gwamnati da suka haɗa da Ƴan Sanda, da Sojoji, zuwa ga Fararen hula.

Ƴan Asalin Jahar Anambra dana yankin Kudu Maso Gabas, sun kasance ƴan ta’addan IPOB ke cigaba tsoratar dasu, wanda suke cigaba da neman raba Ƙasar nan.

Awanni 48 bayan kisan ƴan Arewa ba tare da wani tada yamutsi ba a ranar Lahadi, domin babu wata Jarida ko Kafar Yaɗa Labaru data kawo rahoton wannan kisan, ko kuma yin Allah wadai da kisan daga Jami’an tsaro, ƙungiyoyi akan abinda suke kira “da yin shiru akan abinda bai dame ka ba”.

Kashe Ƴan Arewa da wannan Ƙungiyar ta’addanci tayi, ya biyo bayan kwanaki kaɗan da gano kan Ɗan Majalisar Jahar Anambra da ƴan IPOB suka sace.

Sarkin Hausawan Ƙaramar Hukumar Orunba ta Arewa Alhaji Sa’id Muhammad a jiya, ya koka cewa ƴan Arewa a Jahar Anambra tuni sun yanke shawarar barin Jahar, sakamakon cigaba da yawaitar Kashe masu ƴan uwa da mambobin Ƙungiyar ESN ƙarƙashin IPOB.

A tattaunawar sa da Daily Trust, Muhammad yace kashe mace mai cikin ba wani sabon abu bane tare da ɗiyan ta guda 4, ba sabon abu bane, domin Al’umma da dama an kashe su ta wannan hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram