Tsohon gwamnan jihar Imo kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya bayyana cewa a halin yanzu an yi masa kawanya.
Okorocha, wanda ya zanta da manema labarai a gidansa da ke Maitama da ke Abuja, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a kasar nan da su umarcj jami’an EFCC su bar gidansa.
Dan siyasar ya yi mamakin dalilin da ya sa za a mamaye gidansa a ranar tantance duk masu neman tsayawa takarar Shugaban kasa a jam’iyyar APC, inda ya ce bai taba samun wata gayyata ba ko kuma ya samu sammacin kotu daga kowane bangare.
“Gaskiyar magana, halin da na tsinci kaina babu dadi. A halin yanzu ‘yan sanda da jami’an EFCC na can a harabar gidana kuma suna so su kore ni… An toshe ko Ina na gidan
“Abin da nake nema a yanzu shi ne a ba ni dama in je a tantance ni saboda ni mai neman tsayawa takarar Shugaban kasa ne kuma zabenmu ya zai zo ranar Lahadi. Idan ba a ba ni izinin zuwa wannan tantancewar ba, zan iya rasa damar da nake da shi.
“Ni ba wanda ba a sani ba ne a kasar nan. Ina da adireshi kuma mutane sun san ni Dan kasa ne. Duk abin da ya dace EFCC shi ne ta aiko min da gayyata kuma da farin ciki zan amsa gayyatar su” in ji Rochas.
Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kara karfafa wasu jami’an tsaro da ke ci gaba da killace gidan dan siyasar har zuwa lokacin hada wannan rahoto.