Kada Ku Sake Ku Ɗauki Fansar Kisan Fatima, Muna Bincike Kan Gaskiyar Bidiyon – Buhari

Biyo bayan wani bidiyo da aka yaɗa na wata Fatima, wanda ake kyautata zaton cewa Ƴan ta’addan IPOB suka kashe ta, Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba tayi gargaɗin maida raddi, kashe rayuwar Al’umma, da kuma Ɗaukar Fansa.

A cikin bidiyon da aka yaɗa, an ga Mace mai ciki tare da Ƴaƴan ta guda 4 a cikin jini a Isulo, Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa ta Jahar Anambra.

A cikin sanarwar da Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa kan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu, Fadar Shugaban Ƙasa tace tana bincike akan kisan da IPOB suka yi.

Sanarwar mai taken “Fadar Shugaban Ƙasa tayi gargaɗin ɗaukar matakan gaggawa akan bidiyon.

Sanarwar tace “a yayinda Ƙwararru ke cigaba da tantance gaskiyar bidiyon da ake yaɗa, muna kira ga Al’umma dasu guji yin Kalamai dake da manufar ƙara taɓarɓarewar lamarin Ƙasar nan.

“Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma gargaɗi mutane dasu guji tura bidiyon a Kafafen Sadarwa na Zamani.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kuma yi Allah Wadai da wannan lamari, tare da shan alwashin kamo wanda suka gudanar da haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram