Murtala Garo Ya Ƙaryata Labarin Ficewar Sa APC

Ɗan takarar mataimakin Gwamna a jam’iyyar APC Murtala Sule Garo ya musanta rahoton cewa ya fice daga jam’iyyar APC, bayan da ake zargin rashin jituwa tsakanin sa da Gwamna Ganduje.

Murtala Garo ya shaidawa Guda cikin Radiyon jihar Kano, wanda Wakilin Dimokuraɗiyya ya bibiya cewa, yana nan daram a cikin jam’iyyar APC bai sauya sheƙa ba.

Ya ce “Ƙarya ne, ni yanzu ma (ƙarfe biyu na daren Talata) meeting muke yi da Gwamna, ƙarya ce kawai mutane suke yaɗawa”.

Wannan dai ya biyo bayan rahotonnin da aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa Garo ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP a kafafen sada zumunta.

Murtala Garo wanda shi ne tsohon Kwamishinan ƙananan hukumomi na Kano, na cikin ƴan gabada-gabadai ɗin Gwamna Ganduje.

A baya dai Murtalan ya ajiye muƙaminsa ne domin yin takarar Gwamna, kafin daga bisani jam’iyyar tayi maslaha inda ta tsayar da mataimakin Gwaman mai ci Nasiru Yusuf Gawuna, tare da Murtala Garo a matsayin mataimakin Gwamna a zaben 2023 dake tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram