Pauline Tallen Tace Za’a Kafa Kotun Iyali, Domin Adalci Tsakanin Iyaye Da Yaransu A Jihohi 16

Gabanin bikin ranar yara ta duniya 2022, ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kafa kotunan iyali a jihohi 16, domin tabbatar da adalci ga yara kanana, ko dai a matsayin wadanda aka zalunta ko kuma masu aikata laifuka.

Tallen a wani taron manema labarai a ranar Talata ta ce kafa kotunan iyali ya samo asali ne daga ingantacciyar shawara da wayar da kan jama’a don aiwatar da dokar kare hakkin yara a fadin kasar.

A cewarta, taken wannan shekarar shi ne ‘Karfafa Tsarukan Tallafawa don Kare Yaran Najeriya; tare da bukatar a Farka.’

Tallen ta kuma yi nuni da cewa, duk da kokarin da gwamnati da masu ruwa da tsaki suka yi, har yanzu yara suna cikin mawuyacin hali kuma ana fama da matsalar sace-sace, kashe-kashen al’ada, fyade, auren kananan yara, cin zarafi a gida, da dai sauransu.

“Kafa kotunan iyali a jihohi 16 na tarayya ya samo asali ne sakamakon bayar da shawarwari masu inganci da dorewar.”

Tallen ta kuma bayyana cewa, domin tabbatar da tsaro da kare lafiyar yara, ta kuma sake kafa wata kungiya mai zaman kanta da za ta kawo karshen cin zarafin yara da kuma masu gudanarwa a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram