Babu Shaidar Dake Nuna Ƴan Takarar Jam’iyar APC Na Baiwa Deleget Kuɗaɗe – Abdullahi Adamu

Biyo bayan zargin cin hancin da ake yi tsakanin ‘yan takarar jam’iyyar All Progressives Congress da wakilan jam’iyyar a jihohi daban-daban, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Larabar da ta gabata ya ce babu wata shaida da ke tabbatar da ikirarin.

Adamu, wanda ya karyata wannan ikirari a wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya Lora da cewa ya samu ra’ayin sabanin haka.

A cewarsa, babu wata doka a kasar da ta hana masu neman shugabancin kasar daukar yakin neman zabensu zuwa ga wakilai a fadin kasar.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bayyana cewa ya gano wakilan da suka yi ta kai-kawo ga masu neman takara.

“A yanzu, babu wata doka da ta hana masu son takara ziyartar wakilai omin Neman Goyon bayan su. Ba ni da shaidar cewa masu neman na raba kuɗi ga wakilai. A gare ni wakilai ne ke sayar da lamirinsu kan wanda bai dace ba.

“Ya kamata wakilanmu su sani cewa duk wanda ya raba musu kudi ba zai iya zama dan takarar jam’iyyar da ya dace ba. Ba ya nufin alheri ga kasar. Ba ni da mafita ga matsalar, ”in ji shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram