Osinbajo Yace Rashin Hankali Ne Tsantsa Kisan Harira Da Ƴaƴan Ta 4

 

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana kisan da aka yi wa wata mata mai juna biyu Misis Harira Jubril da ‘ya’yanta a Anambra a matsayin rashin hankali tsantsa, rashin tausayi da kuma wulakanci.

Mataimakin shugaban kasar ya ce matakin zai iya haifar da rikicin kabilanci a fadin kasar nan kuma dole ne kowa ya yi Allah wadai da shi.

Kakakin Osinbajo, Laolu Akande, a wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja, ya ce mataimakin shugaban kasar ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan ganawa da wakilan jam’iyyar All Progressives Congress a Makurdi na jihar Benue.

Ya je Binuwai ne a ci gaba da tuntubar da yake yi a fadin kasar nan da wakilan jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC.

“Abin da ya faru a Anambra tare da kashe wata mata da ‘ya’yanta wulakanci ne agare mu duka.

“Wannan mummunan aiki ne kuma rashin tausayi ne da rashin hankali; kuma ina ganin ya kamata mu yi taka-tsan-tsan, a matsayinmu na masu irin wannan kashe-kashe da ake tafkawa, musamman ma inda a fili yake haifar da irin wannan firgici, bacin rai da haifar da wani yanayi da za mu fara samun rikice-rikicen kabilanci da sauran su.

“Kuma ina ganin tilas ne mu yi taka-tsan-tsan tare da yin Allah wadai da shi cikin kakkausar murya, babu wani uzuri ga komai.

“Bai kamata mu bari wani yanayi ya kai ga mun fuskanci mutanen da za su iya yin irin wannan abu ba.

“Yaya ake kashe mace da ‘ya’yanta? Ina ganin wannan mummunan bala’i ne da kowa ya la’ance shi; Shugaban kasa ya yi magana a kai kuma ina so in hada muryata da sauran wadanda suka fusata gaba daya dangane da hakan,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram