Gawuna Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Gwamnan Jam’iyyar APC a Jahar Kano

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya samu nasarar lallasa abokin hamayyarsa, Sha’aban Ibrahim Sharada da ƙuri’u masu rinjaye a daren jiya Alhamis a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano.

Da yake bayyana sakamakon zaɓen Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na Gwamna, Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura ya ce Gawuna ya samu ƙuri’u 2,289, yayin da Ɗan takarar Sha’aban ya samu kuri’u 30.

Ya kara da cewa jimillar wakilai (Delegates) da su ka gudanar da saben sun kai 2,420, wadanda aka tantance su domin kaɗa ƙuri’un, jimillar kuri’un da aka kada 2,339 ne yayin da kuri’u 20 da ba su inganta ba.

A cewar sa “Ni Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura, Shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwani na Gwamnan Jihar Kano na APC, a madadin kwamitin ayyuka na jam’iyyar mu na Ƙasa da ya ɗora mana alhakin tattara sakamakon zaɓen kuma a kidaya shi.

“Bayan kammala wa, na tabbatar da cewa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da ya samu mafi yawan Ƙuri’u an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.”

“Don haka Gawuna shi ne Ɗan takara ɗaya tilo a jam’iyyar APC a zaɓen Gwamna da za a yi a shekarar 2023 a jihar Kano.”

A nasa jawabin Ɗan Takarar Gwamna na jam’iyyar APC Dr. Nasiru Gawuna ya godewa Allah da ya bashi nasara, ya kuma yaba da goyon bayan Gwamna Ganduje da shugabanin jam’iyyar da wakilan jam’iyyar.

Haka zali, Gawuna, ya yi kira ga ɗaukacin ƴan jam’iyyar da su haɗa ƙarfi da ƙarfe su yi aiki tuƙuru domin samun nasara, ya yaba musu bisa yadda suka gudanar da kansu cikin tsari da kwanciyar hankali a lokacin zaɓen fidda gwani.

A nasa bangaren, Gwamna Abdullahi Ganduje ya yabawa kwamitin zaɓen bisa yadda suka gudanar da ayyukansu na gaskiya da tsari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram