Musa Kwankwaso Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani A APC

Tsohon kwamishinan raya karkara na jihar kano Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya lashen zaben fidda gwani na takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura/Madobi/Garun mallam a majalisar wakilai ta tarayya.

Yayin zaben Musa Iliyasu Kwankwaso ya lashe zaben ne da kuru’u 150, yayin Dan Majalisa Mai Wakiltar yankin ƙananan hukumomin Hon Kabiru Danhassan ya sami kuru’u 4, sai kuma Hajiya Hama Ali Aware Garun mallam ta sami 6.

Musa Iliyasu Kwankwaso dai tsohon Kwamishinan Ma’aikatar raya karkara ne a zamanin mulkin Malam Ibrahim Shekarau da Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Yanzu dai Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso shi ne zai wakilci jam’iyyar APC a Babban zabe Mai zuwa na shekarar 2023, Inda ake ganin Zai iya yin nasara Saboda farin jinin da yake da shi a wurin al’ummar yankin Kura Madobi da Garum mallam.

Yanzu haka dai da dama cikin Kwamishinonin Gwamna Ganduje da suka ajiye Mukaman su, sun kai ga yin nasara a zaben fidda gwani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram