Tsohon shugaban hukumar bunƙasa kanana da matsakaitan masana’antu ta ƙasa, SMEDAN, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa ya lashe zaben fitar da gwani na takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina.
Dikko Radda ya samu ƙuri’u 506 cikin kuri’un ‘delegates’ 1,805 da suka kada a zaɓen da ya gudana a ranar Alhamis a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina.
Daga cikin waɗanda suka tsaya takara a jam’iyyar ta APC sun hada da tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa da ya samu kuri’u 442, da Abubakar Sadiq Yar’adua wanda da ya samu kuri’u 32.
Sauran su ne tsohon kwamishinan kasafin kudi na jihar Katsina Faruq Lawal Jobe da ya samu kuri’u 71, sai Abdulkarim Dauda Daura 07, Abbas Umar Masanawa 436, Umar Abdullahi Tata 08, Alhaji Mannir Yakubu 65, Ahmad Musa Dangiwa 220.