Ƴan bindiga sun hallaka Ango da Amaryar sa mai juna biyu a garin Jere na Ƙaramar Hukumar Kagarko ta Jahar Kaduna.
Ƴan bindigar sun kuma sace iyalan tsohon Kwamishinan Magance Talauci na Jihar Kaduna, Abdulrahman Ibrahim Jere.
Daily Trust ta gano cewa Ƴan ta’addan sama da 50 suka je Jere, wai gari akan hanyar Abuja-Kaduna a saman Babura.
Sun shiga gida-gida, amma an gano cewa sun shiga tsohon Kwamishinan Abdulrahman Ibrahim Jere wanda yabar garin a lokacin.
Haka zalika, sun sace Matar shi da yarinya, ƙaramar ƙannuwar sa da ƴar uwar matar shi.
Hassan Adamu Jere wani mazaunin garin, yace ƴan bindiga sun kai hari a gidan sabbin Ma’aurata, inda suka so sace Ango amma yaƙi, bayan sun sace Amaryar.
A lokacin da yake hana a tafi da Matar shi, shine suka Harbe shi.
Yace akwai rikici a yayinda Matasan garin suka bayyana fushin su cewa duk da Jami’an tsaro na Soji, Yan Sanda, da wasu sauran Jami’an tsaron amma sai da ƴan bindigar suka yi awanni sama da 3.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kaduna ASP Mohammed Jalige bai maida jawabi akan kiran da aka yi mashi ba, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.