Alhassan Ado Doguwa Ya Sake Samun Tikitin Tsayawa Takarar Majalisar Wakilai Karo Na 7 A APC

Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai Alhassan Ado Doguwa ya sake samun Tikitin Tsayawa Takara domin zaben Shekarar 2023.

Doguwa wanda ke wakiltar Doguwa/Tudun Wada a Majalisar Tarayya na Kasa a Jahar Kano, ya samu Tikitin Tsayawa Takara bayan lashe zaben Fidda Gwani da yayi karo na bakwai.

Ya shiga Majalisa tun Jamhuriya ta huɗu, ya kasance mamba tun a lokacin.

An zabi Ɗan Majalisar a shekarar 1992 bayan ya kammala Shirin Yiwa Ƙasa Hidima (NYSC).

Dayake jawabi ga Manema labaru bayan ya samu nasarar zama Ɗan Majalisa yace “wannan shine karo na bakwai, da nake neman Ɗan Takara ba tare da abokin hamayya ba.

Ɗan Majalisar ya yaba da goyon bayan Shuwagabanni da Magoya bayan APC a Mazaɓar shi da Jahar Kano da irin goyon bayan da suke nuna mashi, da kuma yarda da sake Jagorantar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram