Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta cewa ya karbi wasu kudaden cin hanci daga hannun gwamnan Rivers, Nyesom Wike.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Adamu ya fitar a daren jiya Asabar ta ce shugaban jam’iyyar NNPP na kasa ya ji kunya da ikirarin karbar cin hanci.
Ana zargin tsohon Sanatan Kano ta tsakiya da karbar dala 15,000 daga hannun Wike ga kowadanne wakilai na kananan hukumomin 44 na jam’iyyar ta Kano.
Adamu ya tuna cewa Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP a ranar 29 ga watan Maris.
“Abin dariya ne ace dan takarar shugaban kasa zai yaudari shugaban jam’iyyar adawa da kudi domin ya cuci wakilan jam’iyyarsa.
“Mun musanta wannan zarge-zargen. Muna kira ga jama’a da su yi watsi da bayanan karya domin kwata-kwata karya ce kuma yaudara,” inji shi.
Kwankwaso ya shaida wa magoya bayansa da su mai da hankali, su jajirce kuma su yi watsi da “rahotanni da aka dauki nauyin su don lalata” ” farin jininsa na karuwa”.
Wakilan PDP 811 sun kunshi wakilai na kasa daya da aka zaba daga kowace karamar hukuma 774.
Sauran kuma wakilai ne na musamman a kowace jiha da birnin tarayya Abuja da kuma nakasassu.
Kwankwaso wanda tsohon ministan tsaro ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP.
Wike dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar PDP. Ana ci gaba da gudanar da taron a dandalin a Abuja.