Betty Akeredolu, Uwargidan Gwamnan Jihar Ondo, wacce ke neman tsayawa takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a Imo ta yamma , an kore ta daga sakatariyar jam’iyyar da ke Imo a ranar Asabar.
Uwargidan gwamnan Ondo wacce ta fito daga Imo ta jagoranci magoya bayanta dan yin zanga-zanga zuwa sakatariyar APC domin nuna adawa da zabin amincewar yarjejeniyar jam’iyya na zaben dan takararta a zaben 2023.
Rikici ya barke a lokacin da magoya bayanta suka yi kaca-kaca, inda suka dage cewa dole ne a ba su damar kada kuri’a, amma ‘yan sanda sun yi kokarin shawo kan taron.
Ana cikin haka dai an samu turmutsutsu yayin da ‘yan jarida da wakilan da su ma suka isa atisayen suka yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.
‘Yan sandan sun fatattaki uwar gidan Akeredolu da magoya bayanta daga harabar domin ci gaba da zanga-zangar.
Uwar gidan Akeredolu, wanda ta yi wa manema labarai jawabi a kofar sakatariyar, ta ce rashin adalcin da aka yi na bai wa masu son yin yakin neman zabe sai a shaida musu cewa jam’iyyar ta amince da zabin yarjejeniya.
Ta ce, “Dole ne mu yi zaben delegate. Ba zan iya ɓata lokaci da albarkatu wajen yaƙin neman zaɓe ba sai kawai a ce ’yan takara za su fito ta hanyar yarjejeniya.
Dole ne mu kada kuri’a kuma idan na yi rashin nasara, zan amince da sakamakon,” in ji ta.