Shugaban Masu Tsawatar wa na Majalisar Wakilai Ta Ƙasa Orji Kalu yace samun nasarar Atiku Abubakar a matsayin Ɗan Takarar Jam’iyyar PDP ya zama dole Jam’iyyar APC ta zaɓi Dan Takarar APC daga Arewa, idan har Jam’iyyar tana son Cigaba da mulkar Ƙasar a 2023.
Mr Kalu ya bayyana haka a cikin wata sanarwar daya fitar, jim kaɗan bayan PDP ta ayyana Atiku a matsayin Ɗan takara, yana mai cewa dole APC ta fito da Dan Takarar ta daga yankin Arewa maso Gabas domin Atiku daga can ya fito.
Mr Kalu Wanda ya Kasance tsohon Gwamnan Jahar Abia ya nuna son shi na fito da Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan wanda ya fito daga Jahar Yobe Arewa maso Gabas.
Ahmad Lawan yana ɗaya daga cikin ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC.
Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, tsohon Gwamnan Jahar Lagos Bola Tinubu, da kuma tsohon ministan Harkokin Sufuri suna daga cikin manyan Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa a APC.
“Ina taya murna ga PDP data zaɓi Ɗan Yankin Arewa maso Gabas” Mr Kalu ya bayyana haka a cikin sanarwar daya fitar a shafin sa na Facebook.
“Dole Najeriya sun ga abinda na gani a jiya. Domin Jam’iyyar mu ta APC, yanzu babu sauran wata magana ta tsaida Ɗan Takara daga yankin Kudu sai dai in Jam’iyyar na son tayi ritaya daga Siyasa”, Inji shi.
Sanata Kalu yayi kira ga Shuwagabannin Jam’iyyar APC da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari data tilasta APC ta fito da Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa daga yankin Arewa maso Gabas.
“Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana damar da zai fito da wanda zai gaje shi, kuma ina kira a gareshi daya zaɓi Sanata Ahmed Lawan a matsayin magajin shi.
Yayi kira ga Ƴan Takara dasu janye su goyi bayan Ahmed Lawan