Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Rediyo A Anambra, Sun Ƙona Motoci Da Gini

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a safiyar ranar Litinin, sun mamaye harabar gidan rediyon Anambra (ABS), da ke Awada, a tashar Onitsha.

‘Yan bindigar da ake kyautata zaton cewa suna cikin wadanda ke addabar jihar sama da shekara guda sun kona wani gini,da motar bas ta kamfanin, da kuma wata mota da wani ma’aikaci ya ajiye a harabar da ya yi aiki dare.

Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa ba a samu asarar rai ba a harin, amma ‘yan bindigar sun musgunawa ma’aikatan da suka hadu da su a harabar, inda suka yi musu rauni.

Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, wani ma’aikaci da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce jami’an tsaro na yi musu tambayoyi kan harin.

Ya yi alkawarin ba da cikakken bayani kan harin da ‘yan bindigar suka kai musu, kamar yadda ya kwashe dare yana aiki, kuma ya shaida harin.

Anambara, wani kamfani mallakin gwamnatin jihar yana ba gwamnatin jihar goyon baya a yakin da take yi da ‘yan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram