An Canza Takardar Sakamakon Zaɓen FIdda Gwani Na Ɗan Majalisar Tarayya Na Daura – Hon. Fatuhu

Ɗan Majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mai’adua da Daura da Sandamu Hon Fatuhu Muhammad ya ce an canza takardun cike sakamakon zaɓen fidda gwani na Daura (result sheet)

Kamar yadda ya bayyana a cikin wata Sanarwa da ya rabawa manema labarai a Katsina, hon. Fatuhu ya ce an kirkiri sabuwar takardar cike sakamakon ne saboda wata manufa.

Hon. Fatuhu na zargin wasu marasa kishin Daura da kitse wannan badaƙala domin a kayar da shi zaɓe.

Sai dai kuma mun tuntuɓi shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Aliyu JB domin jin yadda takardar sakamakon zaɓen fidda gwani ta Daura ta sha babban da ta sauran wurare a faɗin jihar Katsina.

Alhaji Sani JB ya bayyana cewa ba jami’yya ba ce a mataki jiha ta shirya wannan zaɓe ba, kuma an turo kwamiti da zai saurari koken duk wanda ke da wani korafi.

Tuni dai Hon Fatuhu Muhammad ya aike da wannan korafi na shi zuwa ga kwamitin da uwar jam’iyyar APC ta turo daga Abuja domin sauraren koke-koken jama’a akan zaɓen fidda gwani na ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar juma’ar da ta gabata.

Abin jira a gani shi ne, wane irin mataki wannan kwamiti zai ɗauka akan masu koke dangane da yadda aka gudanar da wannan zaɓe da wasu ke ganin ba a yi masu adalci ba, lokaci zai nuna.

Daga ƙasa takardu ne guda biyu ɗaya sakamakon zaben fidda gwani ne da aka gudanar a ƙaramar hukumar Katsina ɗaya kuma wanda ake koke ne akan sa da aka gudanar a ƙaramar hukumar Daura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram