An Haramtawa Ƴan Jarida Shiga Ɗakin Taro, Yayin Da APC Ta Fara Tantance Ƴan Takarar Shugaban Ƙasa

An Haramtawa Yan jarida Shiga Dakin Taro, Yayin Da APC Ta Fara Tantance Yan takarar Shugaban Kasa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara tantance masu neman tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Ana gudanar da tantancewar ne a otal din Transcorps Hilton da ke Abuja.

Tun da farko an shirya tantancewar a ranar 23 ga Mayu, 2022, amma kwamitin zastaswa (NWC) ya dage shi.

Sai dai an hana ‘yan jarida shiga dakin taro na Transcorps Hilton inda ake ci gaba da tantancewar.

Sai dai wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa tsohon karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ne aka fara tantance shi.

Sai dai ya ki yin magana da manema labarai lokacin da ya sauko daga benen.

Wadanda za a tantance su ne; Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba; tsohon ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio; Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun; Gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi; tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Sauran sun hada da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan; Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi; Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru; Fasto Tunde Bakare; Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade; tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sani Yarima, tsohon ministan yada labarai, Ikeobasi Mokelu da mace mai neman takara, Uju Ohanenye; Nicholas Felix; tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole; Tein Jack-Rich da wasu ‘yan kaɗan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram