Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da ɗan takarar gwamnan jahar Katsina na shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Dikko Umar Raɗɗ a ranar Litinin ɗinnan a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.
Dikko Raɗɗa ya ziyarci shugaba Buhari ne tare da gwamnan jahar Aminu Bello Masari.