Hukumar NECO Ta Ƙara Wa’adin Yin Rajistar Jarabawar SSCE 2022

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (NECO) ta kara wa’adin yin rijistar jarrabawar kammala makarantun sakandare ta shekarar 2022 (SSCE).

Yanzu ana iya yin rijista har zuwa tsakar daren ranar Litinin, 20 ga watan Yuni.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a Azeez Sani ya fitar da sanarwa a ranar Litinin.

Tun da farko dai an shirya rufe lokacin rajistar ne a ranar Litinin 30 ga watan Mayu.

An sanar da Ma’aikatun Ilimi na Jihohi, Shugabanni, Kwamandoji da duk masu ruwa da tsaki cewa ba za a sake kara wa’adin ba.

Jarabawar NECO ta SSCE 2022 za ta fara ne a ranar 27 ga watan Yuni kuma za kammala a ranar 12 ga watan Agusta.

Sanarwar ta kara da cewa, za a yi wa ‘yan dalibai jarabawar ne a darussa 76.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram