Sojojin Ƴan Awaren Ambazoniya Sun Hallaka Mutane 20 A Jihar Cross River

Akalla ‘yan kasar Kamaru 20 ne sojojin Ambazoniya da ke fafutukar kwato ‘yancin kai a yankin Kudu maso yammacin Kamaru suka hallaka.

Shaidun gani da ido a kauyen Boki da ke Najeriya sun ce sojojin Ambazoniya sun tsallaka cikin al’ummar Najeriya da ke kusa da Bashu a karamar hukumar Boki ta jihar Kuros Riba domin kai farmaki kan ‘yan uwansu da suka gudu suka ki shiga tare da su domin zafafa yaki kan gwamnatin shugaban kasa Kamaru Paul Biya.

Cletus Obun, wanda ya taba zama dan majalisar dokokin jihar Cross River, kuma dan takarar majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Boki/Ikom, ya tabbatar da faruwar lamarin.

“Zan iya tabbatar da cewa sojojin Ambazoniya sun tsallaka kan iyakar Najeriya da safiyar Lahadi domin kai farmaki ga ‘yan uwansu da suka tsere zuwa Najeriya suka ki shiga sojojinsu don yaki.

“Sun kashe kusan Mutane 20 sannan Babu wanda ya tabbatar har yanzu idan a cikin wadanda aka kashe, akwai ‘yan Najeriya.

A cewar Cif Obun, sauran ‘yan kasar Kamaru da ke cikin al’ummar da ke magana da harshen Bokye na ‘yan kabilar Boki na Najeriya, yanzu haka sun mamaye al’ummar Bashu da ke kusa da garin Danare inda sojojin Najeriya ke da wani karamin sansani.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na Brigade 13 na Sojojin Najeriya dake Calabar, Captain Tope Aluko, ya ce ya tuntubi jami’insu na Officer Operation, inda ya ce ba su samu irin wannan rahoton ba.

Shima Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Emmanuel Bwacha, ya koka kan yadda wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne ‘yan kasar Kamaru su ka bindige Dagacin kauyen da wasu mazauna garin Manga a jihar Taraba.

Dan majalisar dai ya ce ‘yan awaren Kamaru sun rusa kauyen.

Bwacha, mai wakiltar Taraba ta Kudu a majalisar dattawa, ya ce mamayewar ‘yan awaren na barazana ga yankin Najeriya saboda har yanzu ba a san dalilinsu ba.

Ya ce, “Na tashi da safen nan ne domin in jawo hankalin mutanen kasarmu musamman jami’an tsaro kan wannan mummunan lamari da ke kawo mana cikas da ci gaban kasarmu. Karamar hukumar Takum tana dauke da bataliya ta 23 ta sojojin Najeriya, don haka mai girma shugaban kasa, mika wuya na ne cewa sojojin Najeriya su tashi tsaye wajen dakile wannan bala’in da ba a taba gani ba.

“Har yanzu ba a san manufar (‘yan aware) ba, ko suna son fadada yanki ko kuma neman yankin Kudu maso yammacin Kamaru.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram