Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya tuhumi tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da sauran shugabannin jam’iyyar PDP da su ci gaba da mai da hankali kan yunkurin ruguza jam’iyyar APC mai mulki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sahannun mai magana da yawun sa, Nathaniel Ikyur ya fitar, yayin da yake taya Atiku murnar lashe tikitin takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa.
A cewar Ortom, nasarar da Atiku ya samu a babban taron jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar Asabar a Abuja, nasara ce Daga Allah.
Ya bayyana zaben fidda gwanin da aka gudanar cikin lumana, inda ya yabawa duk masu son tsayawa takara, musamman gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da sauran wadanda suka halarci zaben.
Ya ce, “A cikin Yohanna 3:27, Littafi Mai Tsarki ya ce, ‘Mutum ba zai iya samun kome ba, sai an ba shi daga sama.” Don haka, don amfanin duk ’yan Najeriya da muke ƙoƙari don inganta al’umma, Ina kira ga shugabancin jam’iyyar da mu mayar da hankali wajen ganin mun kawar da jam’iyyar APC da ta ruguza ainihin al’ummarmu, ta hanyar cin zaben 2023 domin dawo da martabar ‘yan Nijeriya a gida da waje.”
Ortom ya yi kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar masu kishin kasa da su kasance da hadin kai a yunkurinsu na karbar madafun iko a dukkan matakan gwamnati ta hanyar zaben 2023.