Kotu Ta Tsare Wani Mutum, Bisa Zargin Garkuwa da Yiwa Yar Dan Uwansa Fyade

Kotu Ta Tsare Wani Mutum, Bisa Zargin Garkuwa da Yiwa Yar Dan Uwansa Fyade

Rundunar ‘yan sandan jihar Binue a ranar Litinin ta gurfanar da wani Kakule Aondonyega (18) a gaban wata kotun yankin Makurdi bisa laifin yin garkuwa da wata karamar yarinya da kuma yimata fyade.

Mai gabatar da kara, Insfecta Rachael Mchiave, ya shaidawa kotun cewa an shigar da karar ne a sashen binciken manyan laifuka (CID), dake Makurdi, ta wata rubutacciyar koke ta wata Dorcas Wajir.

Insfecta Mchiave ya ce mai shigar da kara ya yi zargin cewa a ranar 3 ga Mayu, Kakule Aondonyega na yankin Agina, a garin Zaki-Biam, dake karamar hukumar Ukum , ya yi garkuwa da ‘yar wansa, Dooshima Wajir, karamar yarinya, daga garin Tiontyu, karamar hukumar Tarka, inda take zaune tare da ‘yar uwarta, Jennifer. Wajir, ya kai ta wurinsa a Zaki-Biam ya yi lalata da ita.

Mai gabatar da kara ya ce yayin binciken ‘yan sanda, Aondonyega ya amsa laifinsa.

Alkalin kotun, Mrs Dooshima Ikpambese, ta bada umarnin tasa keyar wanda ake tuhumar zuwa a gidan yari na tarayya dake Makurdi, sannan ta sanya ranar 30 ga watan Yuni domin ci gaba da ambatonsa. (NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram