Kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar PDP ya gabatar da takardar shaidar cin zabe ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Mista Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ne a yayin babban taron jam’iyar kasa na musamman da aka gudanar a Abuja a ranakun 28 da 29 ga watan Mayun 2022 bayan ya samu kuri’u 371 inda ya doke wasu ‘yan takara 11 a suka fafata a zaben
Gwamnoni, ’yan takarar gwamna, ’yan takarar shugaban kasa, mambobin kwamitin amintattu na BoT, ‘yan majalisar wakilai ta kasa, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar da duk masu ruwa da tsaki ne suka halarci bikin na musamman.
An gudanar da taron ne a ranar Laraba a sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa da ke Abuja