Kuri’a Ce Zata Tantance Wanda Zai Lashe Zaben 2023, Ba Kafofin Sada Zumunta Ba – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa a ta bayyana fargabar da take game da zabukan 2023, bayan da katunan zabe miliyan 20 na dindindin da aka ce suna ajiye ba tare da an karba ba.

Hukumar ta kuma yi Allah wadai da yadda ‘yan kasar ke nuna ko’in kula wajen yin rajistar zabe domin su kada kuri’a a zabe mai zuwa.

Mataimakiyar daraktar hukumar ta INEC, Mary Nkem, ta bayyana hakan yau a Abuja, yayin kaddamar motar tafi da gidanka domin samar da katin zaben, wanda wata kungiya mai zaman kanta, mai suna ”Advocacy for Civic Engagement” ta shirya.

A don haka ne ta yi kira ga ‘yan Najeriya musamman matasa da su ba da himma wajen zaben sabbin shugabannin da za su kawo sauyi na gaskiya da kuma ciyar da kasa gaba.

A cewarta, kuri’u ne ba kafofin sada zumunta ba ne za su tantance wadanda suka lashe zaben 2023.

Nkem ta ce, “aikin samar da katin zaben ta internet ya fara ne a ranar 30 ga Yuni 2021; amma mun gano cewa tsakanin wancan lokaci zuwa ‘yan makonnin da suka gabata, an samu raguwar fitowar jama’a.

“Idan har matasan kasar nan za su fito gaba daya domin kada kuri’unsu, to ba za mu sake yin zaben kashi 15 ko 20 cikin 100 na masu kada kuri’a ba, domin mun san cewa yawan matasa ne kadai zai iya kawo sauyi.

Babban Daraktan kungiyar Obinna Osisiogu ya bayyana cewa, aikin yawo da motar domin samar da katin na PVC zai tallafawa akalla kashi 60 cikin 100 na matasan da suka cancanci kada kuri’a su yi rajista da karbar katin zabe na dindindin da kuma kada kuri’a a zaben 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram