Ministan Lafiya Yace Yawan Jama’a Na Yin Illa Ga Ci gaban Su

Yawan Jama’a Na Yin Illa Ga Ci gaban Su—-Ministan Lafiya

Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya ce karuwar al’ummar Najeriya na yin illa ga ci gaban zamantakewa a kasar tare da illa ga samun rayuwa Mai ingancin.

Ya yi wannan jawabi ne jiya a Abuja a wajen kaddamar da rahoton yawan jama’a na duniya na shekarar 2022 wanda asusun kula da yawan al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya, mai taken ‘Ganin abun ake boye: gami da yin Aiki cikin Rikicin da Ba a sanda shi ba.

Ministan Lafiyan, Osagie Ehanire, a lokacin da yake jawabi, ya ce yawan al’ummar Najeriya a halin yanzu, ana hasashen zai kai kimanin miliyan 214 saboda yawan karuwar al’umma da kashi 3.2 bisa 100 da kuma yawan haihuwa da ka samu na kashi 5.3 cikin 100 na yara. ya kara da cewa “rashin amfani da tsarin iyali bai dace ba.”

Shi ma da yake nasa jawabin, shugaban hukumar kidaya ta kasa, Nasir Isa Kwarra, ya ce miliyan 2.1 na masu juna biyu a Najeriya, sun dauke shi ne batare sun Sani ba.

A cewarsa, galibin mata da ‘yan mata suna samun kansu a cikin yanayi da zai hana su aiwatar da muhimman hakkokinsu da kuma samun damar yanke shawara kan batutuwan da suka shafi rayuwarsu ta haihuwa.

Ya Kuma ci gaba da cewa, karancin yawan jama’a na da sakamako Mai kyau akan lafiyar jama’a, jin dadin su, burinsu anan gaba, samun kudin shiga, Samar da tsaro, da aiki yi, burinsu, samun ilimi da dai sauransu.

Wannan dai na zuwa ne yayin da Wata kungiya mai zaman kanta mai suna “Plan International” ta ce sama da ‘yan mata da mata miliyan 37 a Najeriya ba sa samun kayayyakin tsaftar al’ada saboda tsadar rayuwa.

Charles Usie, daraktan kungiyar Plan International a Najeriya ne ya bayyana hakan a Abuja, a jiya talata a taron masu ruwa da tsaki na tunawa da ranar tsaftar jinin al’ada ta 2022.

Taken taron dai shi ne ‘batutuwa kan Al’ada”:

Sai dai Usie ya yi kira da a samar da na’urar tsaftace muhalli kyauta ga ‘ya’ya mata masu tasowa domin samun ingantacciyar kulawar al’ada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram