Cibiyar Kula da dakile Cututtuka masu yadawa ta kasa (NCDC) ta ce Najeriya ba ta da dakunan gwaje-gwaje da ake amfani dasu wajan samar da cutar Kyandar Biri.
Darakta-Janar na NCDC, Ifedayo Adetifa, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da yake mayar da martani ga rahoton da, babban jami’in hukumar kula da Sinadai da Kariyar yaduwar Halittu na Rasha ya fitar.
Da yake mayar da martani ga wani rahoto da aka ce babban jami’in hukumar na Rasha ya fitar, Daarakta Janar na Hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce an sanar da shi ayyukan dakunan gwaje-gwajen lafiyar al’ummar Najeriya. ga hukumomin da ke sa ido, yawancin dakunan gwaje-gwajen da Gwamnatin Tarayya ta kafa su a duk Jihohi 36 dababban Birnin Tarayya Abuja, don dalilai na bincike, da kuma magance cutar COVID-19 da sauran cututtuka masu yaduwa.
Rahoton ya yi zargin cewa “akwai dakunan gwaje-gwajen halittu da kasar Amurka ke sarrafawa a Najeriya”.
Da yake mayar da martani ga wata sanarwa da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar na cewa, kwayar cutar ta Kyandar biri da ke haddasa bullar cutar a Turai da sauran wurare an shigo da su ne daga Najeriya inda Amurka ta tura kayayyakin aikinta, NCDC ta ce sanarwar ba ta da tushe balantana makama.
Ta ce a bisa ka’ida, Najeriya na maraba da hadin gwiwar kimiyya da dukkan kasashen waje, kuma ta samu tallafin kayan aiki daga Burtaniya, Jamus, Japan da sauransu, kuma ta tattauna batun samar da alluran rigakafin tare da kasar Rasha.
Hukumar yaki da cututtukar ta kara da cewa, hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka ya samar da damammaki na a fannin fasaha, inganta gudanar da aiki, samar da kayan aiki da asibitocin, a daidai lokacin da annobar COVID-19 ke yaduwa, da kuma kudade don tallafawa shirye-shiryen kiwon lafiya, kamar na magance cutar Soda wato HIV ko AIDS, kawar da zazzabin cizon sauro, da dai suran su.
The disease control agency added that, collaboration between Nigeria and the United States had provided opportunities for technical assistance, capacity building, provision of equipment and field hospitals at the peak of the COVID-19 pandemic, and funds to support health programmes, like HIV/AIDS, malaria elimination.