Wasu ƙasashen duniya 44 ciki harda Najeriya na fuskantar matsalolin tsadar abinci sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, a cewar wani kamfanin bincike na Boston, BCG mai nazari kan lamura a duniya.
Kamfanin na BCG da ya fitar da rahotonsa mai taken ‘Yaƙin Ukraine da turmutsitsi ciyar da duniya’, ya magantu dalla-dalla kan tasirin yaƙin Ukraine kai-tsaye ga matsalolin abinci a duniya.
BBC Hausa ta ruwaito cewa, Rahoton ya ce ƙasashen da ke cikin wannan akuba ban da Najeriya da sauran yankunan Afirka akwai Kudancin Asiya da Latin Amurka.
BCG ya kuma ce akwai damuwa matuka musamman ga Najeriya da tattalin arzikinta ke cikin wani yanayi ga kuma tasirin da annobar korona ta yi wajen sake kassara kasar.
Hakazalika an kiyasta cewa mutane biliyan 1.7 daga kasashe masu tasowa za su fuskanci matsananciyar yunwa da karuwar farashin makamashi da basuka a cewar Majalisar Dinkin Duniya.