Majalisar dokoki ta dakatar da ciyamomin Ƙananan Hukumomi 2 a Kaduna
Majalisar dokokin Jihar Kaduna ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi guda biyu saboda zargin kashe kudade babisa ka’ida ba.
Shugabannin kananan hukumomin su ne Salasi Musa shugaban karamar hukumar Chikun da Abubakar Lawal na karamar hukumar Giwa.
Dan majalisar dake wakiltar Zaria Kewaye Alhaji Ahmed Chokali ya gabatar da kudirin dakatar da shugabannin biyu yayin zaman majalisar.
Ya ce majalisar ba za ta lamunci yanda mutanen ke karya ka’idojin gudanar da kananan hukumomi ba don haka za ta gudanar da bincike akansu.
Nan take shugaban Majalisar, Alhaji Yusuf Zailani ya umarci kwamatin kula da kananan hukumomi na majalisar ya gudanar da bincike tare da gabatar da rahotansa ga ‘yan majalisa.