Waiwaye: Yadda Atiku Yayi Fatali Da Dokar Hana Kiwo A Fili

Waiwaye: Yadda Atiku Yayi Fatali Da Dokar Hana Kiwo A Fili

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar, a ranar 31 ga watan Junairun shekarar 2019 ya yi fatali da dokar hana kiwo asarari da aka kafa a wasu jihohin kasar nan.

Atiku, wanda ke amsa tambayoyi kan tattaunawar da aka yi a wata daya gabanin zaben shekarar 2019 mai suna “The Candidates”, ya ce dokar ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar, kuma ta tauye hakkin Fulani makiyaya na ‘yancin walwala da zama a fadin kasar nan.

Dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ya bayyana cewa ba za a iya bin dokar ba.

Ya ce, “Dole ne mu duba yadda waɗannan dokokin suka kasance cikin tsarin mulki. Ban tabbata ba ko sun zo ne da tanade-tanaden kundin tsarin mulkinmu wanda ya ba da ’yancin yin tafiya, ’yancin zama a duk inda kuke so a cikin ƙasa da sauransu, Don haka dole ne mu kalli hakan

Kundin tsarin mulkin kasar bai hana zirga-zirgar jama’a a Najeriya ba, don haka duk wata doka da ta hana mutane tafiya cikin walwala da gudanar da harkokinsu na halal ba za a iya kiyaye su ba”.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wasu daga cikin gwamnonin da suka rattaba hannu kan kudirin dokar haramta kiwo asarari a jihohinsu daban-daban a halin yanzu suna goyon bayan Atiku ya zama shugaban kasar Najeriya.

Baya ga jihar Binuwai da ke Arewa ta Tsakiya, kimanin jihohi bakwai na Kudancin kasar nan har da Legas ne suka kafa dokar.

Jihar Ekiti ta sanya hannu kan dokar hana kiwo a fili a shekarar 2016, ta bada damar daurin akalla watanni shida a gidan yari ga wadanda suka gaza bin dokar.

Jihar Abia ma ta sanya hannu a kan nata a shekarar 2018, yayin da Gwamnan Bayelsa Douye Diri ya sanya hannu kan dokar a watan Maris na 2021, inda ya bayyana cewa abin da ake so a yi shi ne a dakatar da rikicin makiyaya da manoma a jihar.

Ku tuna cewa Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya sanya hannu kan kudirin dokar a watan Agustan shekarar 2021.

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel a lokacin da ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili a watan Satumban shekarar 2021, ya ce kiwo a fili ya shafi ci gaban jihar.

Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi shi ma ya sanya hannu kan dokar a ranar 15 ga watan Satumbar shekarar 2021.

A halin da ake ciki, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe da takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, sun sha alwashin marawa Atiku baya na tsayawa takarar shugaban kasa da kuma tabbatar da ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram