Da Dumi-dumi: APC Ta Kori Mutane 10 Dake Neman Takarar Shugabancin Kasa
Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan Yuni, jam’iyya mai mulki tace masu neman tsayawa takara shugaban kasa 10 ne basu can canta ba.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa Shugaban Kwamitin tantance masu neman tsayawa takarar Shugaban kasa kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Cif John Oyegun ne ya bayyana haka a yau Juma’a a Abuja lokacin da ya mika rahoton kwamitin ga jam’iyyar.
Har yanzu ba a bayyana sunayen masu neman tsayawa takarar da basu can canta ba.