Fashewar Tukunyar Gas Ya Jikkata Mutane 20 Tare Da Ƙona Shaguna A Kano

Fashewar Tukunyar Gas Ya Jikkata Mutane 20 Tare Da Ƙona Shaguna A Kano

Fashewar tukunyar iskar gas a wani kanti ya yai sanadiyar raunata mutane a ƙalla ashirin da kuma kona shaguna a Kano.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a wata unguwa mai cunkoso a unguwar Sheka, Karshen-Kwalta a a cikin birnin Kano.

NAN ya tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na daren jiya Alhamis, inda wata tukunyar gas ta fashe kuma nan take ta kama wuta.

Gobarar ta lalata wasu shaguna kusan uku da ke kusa, ciki har da wani bangare na wani gida da ke daura da shagon.

Shaidu sun shaida wa NAN cewa sun ji karar fashewar tukunyar gas ɗin.

Wani mai suna Malam Abubakar, ya ce an garzaya da mutane da dama asibiti tsirara, dauke da ƙunar wuta a jikinsu.

Ya ce sama da mutane 10 ne lamarin ya rutsa da su, akasari wadanda ke cikin shagon ne da kuma mutanen da ke kusa da wurin da suke sana’arsu.

Da NAN ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce mutane 20 ne ke da hannu a lamarin, amma an ceto su da ransu, kuma yanzu haka suna samun kulawa a asibitoci.

Yusif ya ce lamarin ya faru ne sakamakon gobara da wani mutum mai soya da kuma sayar da kifi a kusa da shagon gas din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram