FCT Zata Kashe Biliyan 1 Domin Gyaran Babban Masallacin Abuja, Da Coci

FCT zata Kashe Biliyan 1 domin gyaran Babban Masallacin Abuja, da Coci

Birnin Tarayya Abuja ya fara tattara kuɗaɗen Shiga da Yawun yakai sama da Naira biliyan 200 duk shekara ta hanyar shirin ta na karɓar Kuɗaɗen Haraji.

Ministan Abuja Muhammed Bello ya bayyana haka a ranar Alhamis a lokacin da yake jawabi a taron da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Sadarwa ya shirya a Villa, Abuja.

Yace yanzu Abuja itace ta biyu wajen tattara kuɗaɗen shiga, tana son taga ta wuce Lagos wanda itace Jahar data fi samun kuɗaɗen shiga a Ƙasar.

Yace kimanin Naira biliyan 1 (Naira Miliyan 500 ga kowa) an sanya shi ne domin sake gina Babban Masallaci na Kasa, da Cibiyar Kiristoci ta Kasa, domin su zamanto da za’a riƙa ziyarta ga masu zuwa a Birnin Abuja.

Ya ƙara dacewa yana kuma gyara Sakatariyar Ƙasa da Kuma Majalisun Kasa, yana mai cewa yana yin yadda suke zama dole a canja shi.

Akan tsaro, wanda wani gini da ba’a kammala ba ya haifar da Fashewar wani abu, yana gwamnati na bakin Ƙoƙari akan hakan.

Akan rukunin gidajen da babu kowa a Abuja, yace wasu sun gina gidaje ne wajen gari saboda faɗaɗa garin domin karɓar kudin haya kaɗan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram