Goodluck Baya Cikin Waɗanda Aka Tantance Domin Tsayawa Takarar Shugaban Ƙasa – Jam’iyar APC

 

Kwamitin tantancewar na jam’iyyar a ranar Juma’a ya musanta batun tantance tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Shugaban kwamitin tantancewar, John Odigie-Oyegun, ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abduallahi Adamu, a wani taron kwamitin ayyuka na kasa.

Odigie-Oyegun ya shaidawa manema labarai cewa sabanin labaran da ake yadawa, tsohon shugaban baya daga cikin masu zuwa Transcorp Hilton domin atisayen.

Bayanin Oyegun ya biyo bayan rahotannin da ke cewa jam’iyyar ta yi watsi da jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa 23 na jam’iyyar APC zuwa 13.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram