Gwamna Bala Mohammed Ya Sake Naɗa Kashim A Matsayin SSG, Bayan Ya Bar Mashi Takarar

Bayan Janye Takarar sa a Zaɓen Fidda Gwani: Gwamna Bala Mohammed ya sake naɗa Kashim a matsayin SSG

Gwamnan Jahar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a ranar Alhamis ya sake naɗa tsohon Sakataren Gwamnatin Jahar Barista Ibrahim Mohammed Ƙashim a matsayin sabon SSG.

Kashim dai ya ajiye mukaminsa a watan Mayu domin neman Takara biyo bayan umarni da Gwamnan ya bayar ga dukkanin masu riƙe da maƙaman Siyasa dasu ajiye biyo bayan sabuwar Dokar Zaɓe.

A cikin wata sanarwa da Mai ba Gwamna Shawara ta Fuskar Kafafen Yaɗa Labaru na Gwamnan Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana wa Manema Labaru, yace sake naɗa shi zai fara aiki nan take.

“Sanata Bala Abdulkadir Mohammed Gwamnan Jahar Bauchi ya amince da sake naɗa Barista Ibrahim Mohammed Kashim a matsayin Sakataren Gwamnatin Jahar Bauchi.

“An sake naɗa shi saboda nasarorin daya cimmawa, da biyayya, da Jajircewa, gami da gogewa, da ilmi wajen gudanar da aikace-aikacen sa.

“Barista Ibrahim Mohammed Kashim shine Sakataren Gwamnatin Jahar daya sauka.

Daily Post ta bada rahoton cewa Kashim yayi takarar a zaɓen Fidda Gwani na Gwamna a Jam’iyyar PDP a satin daya gabata, kuma ya samu nasara domin tunkarar Babban zaɓe na Shekarar 2023.

Kwanaki kaɗan bayan ya samu nasara a zaɓen, Kashim ya ajiye Takarar shi, yana mai umartar Jam’iyyar data sake sabon Zaɓen Fidda Gwani a ranar Asabar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram