An canza matsayin assibitin ƙwararru ta Medical Centre da ke Katsina zuwa assibitin koyarwa na gwamnatin tarayya, wato Federal Teaching Hospital Katsina.
Shugaban assibitin, Dr, Suleiman Bello Mohammed ya sanar da hakan a wajen wani taron ƴan jarida da ya gudana a ɗakin taro na assibitin a ranar Larabar nan.
Dr, Bello ya ce an ɗaga darajar assibitin ne domin ta zama wurin da ɗaliban koyon aikin likita na jami’ar Umaru Musa Ƴar’adua za su rinƙa gudanar da karantun zahiri wato practical.
Ya ce kafin ɗaga darajar asibitin yana da ƙwararrun likitoci da kayan aiki iri-iri na zamani da ba a cika samunsu a assibitocin Najeriya ba, ya ce wannan ya sanya ma har a ke turo marasa lafiya zuwa assibitin daga assibitin ABU da ke Zaria da assibitin Aminu Kano da ke Kano da sauran manyan asaibitocin ƙasar.
Ya bayyana cewa a halin yanzu akwai likitocin da ke karɓar horon ƙarin ƙwarewa a fannoni daban daban ciki da wajen Najeriya.